Yanzu-yanzu: Hankali mutan Maiduguri ya tashi yayinda ake artabu tsakanin Boko Haram da Sojoji

Yanzu-yanzu: Hankali mutan Maiduguri ya tashi yayinda ake artabu tsakanin Boko Haram da Sojoji

A Yanzu haka, yan kungiyar Boko Haram sun kai hari birnin Maiduguri kuma suna artabu da rundunar sojojin Najeriya.

Yan Boko Haram din sun shigo ne ta hanyar Damboa; wani wuri da akafi sani da wajen Polo.

A yanzu haka mazauna garin sun guduwa daga muhallansu domin kare rayukansu. Wannan harbe-harbe ya fara ne misalin karfe 6 na yammacin yau Alhamis kuma har yanzu ana yi. Misalin karfe 6:15, an jin karan tashin Bam.

Hukumar sojin Najeriya ta sakin jawabin cewa ta dakile wannan hari da yan Boko Haram suka kawo.

Kana ta bukaci mutan Maiduguri sun kwantar da hankulansu yayinda hukumar na dukkan abinda zata iya domin kwantar da kuran.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng