A kowacce shekara, kasar nan na asarar N136b ga makwabta saboda tsafta da tsarin gabar ruwansu

A kowacce shekara, kasar nan na asarar N136b ga makwabta saboda tsafta da tsarin gabar ruwansu

- Kasashen dake da makwabtaka da Najeriya na samun garabasa saboda rashin iya aikin mu

- Masu shigo da kaya sukan gwammace sun hiddo su ta makwabta sai su tuko su ta iyakoki

- Wasu lokutan kuma kayan an hana shigo dasu, don haka sai abi dasu ta barauniyar hanya

A kowacce shekara, kasar nan na asarar N136b ga makwabta saboda tsafta da tsarin gabar ruwansu
A kowacce shekara, kasar nan na asarar N136b ga makwabta saboda tsafta da tsarin gabar ruwansu

Kiris da Najeriya ta rasa jiragen ruwa na daukar kayan makuden kudi har Naira biliyan 136 duk shekara ga kasashen Afirka ta yamma wadanda take makwaftaka dasu kamar su Ghana, Togo da Ivory Coast.

A bisa bincike an gano cewa wannan asarar ta biyo bayan barin kayan da ake yi a tashoshin jiragen ruwan tare da tituna marasa kyau da suke rufe tashoshin jiragen ruwan.

A wasu kasashen jiragen ruwa sukan dau awoyi kadan ne a tashoshin jiragen kafin kafin a bi hanyoyin da suka dace don fitar da kayan da suka zo dashi.

DUBA WANNAN: Hanyoyi 4 na kare kai daga cutukan saduwa

Kafin a waskar da kayan, Najeriya tanada metric tonnes miliyan 10 na cargoes, amma a halin yanzu, metric tonnes miliyan 4.3 na cargoes din aka kai jamhuriyar Benin.

Masu shigowa da kaya cikin gida Najeriya sun shigar da cargo mai metric tonnes miliyan 2.5 kasar Togo, metric tonnes miliyan 1.8 zuwa Ghana da metric tonnes 400,000 zuwa Ivory Coast.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel