An sake dage taron FAAC saboda kasa da kudaden shiga daga sayar da danyen mai suka yi

An sake dage taron FAAC saboda kasa da kudaden shiga daga sayar da danyen mai suka yi

- Kudin da FFAAC ke rabawa ya ta'allaka ne da nawa NNPC ta tara daga sayar da mai

- FAAC ke ware yadda jihohi da tarayya da ma kuma kananan hukumomi zasu sami kudin

- Wasu jihohin bassu da katabus sai sun sami wannan kudi daga Tarayya

An sake dage taron FAAC saboda kasa da kudaden shiga daga sayar da danyen mai suka yi
An sake dage taron FAAC saboda kasa da kudaden shiga daga sayar da danyen mai suka yi

An sake dage taron FAAC saboda kasa da kudaden shiga daga sayar da danyen mai suka yi
An sake dage taron FAAC saboda kasa da kudaden shiga daga sayar da danyen mai suka yi

Wata na biyu kenan da ake tsara taron Federal Account Allocation Committee amma ana fasawa sakamakon munin kudin shiga daga matatar man fetur ta kasa.

Shugaban finance commissioners forum na FAAC, Yunusa Mahmoud wanda ya tabbatar da fasa taron ranar laraban bai fadi takamaiman ranar da za'ayi taron ba.

Mista Mahmoud ya nuna damuwarshi na fasa taron kwamitin sakamakon kudin shiga na matatar man fetur ta kasa yayi kadan ga sashi uku na Gwamnatin.

"An fasa taron sakamakon kalubalen da muke fuskanta" Mista Mahmoud yace.

"Kudin shigar da muka samu daga matatar gaskiya tayi kadan da yanda muke tsammani."

A watan Maris ne aka samu makamancin cigaba irin wannan wanda ya kawo hargitsi, domin wakilan jihohi 36 na kasar da na birnin tarayya sun tashi taron a fusace.

DUBA WANNAN: Obasanjo ya sake sa kafa ya tadiye Buhari a kasar Igbo

Hargitsin ya kawo karshe bayan taron gaggawa da ministan kudi da shugaban FAAC Kemi Adeosun suka kira washegari a inda ya roki wakilan da a raba kudin da matatar ta kawo.

A karshen taron sun yarda da rabon Naira biliyan 647.39 na watan fabrairu da kuma cikon Naira biliyan 100 da aka biya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel