Cece-kuce ya barke tsakanin Donald Duke tsohon gwamna da Okonjo Iweala, tsohuwar Minista

Cece-kuce ya barke tsakanin Donald Duke tsohon gwamna da Okonjo Iweala, tsohuwar Minista

- Tsohuwar ministan kudi, Ngozi Okonjo Nweala ta kalubalanci tsohon gwamnan jihar Rivers, Donald Duke

- Okonjo Nweala tace a littafinta, Duke ya shawarce ta da kada ta karbi mukamin sa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bata

- Tsohon gwamnan jihar Rivers din ya maida martani ga tsohuwar ministan kudin bisa ikirarin da tayi a littafin nata

Cece-kuce ya barke tsakanin Donald Duke tsohon gwamna da Okonjo Iweala, tsohuwar Minista
Cece-kuce ya barke tsakanin Donald Duke tsohon gwamna da Okonjo Iweala, tsohuwar Minista

Legit.ng ta gano cewa a littafinta mai suna "Yaki da rashawa akwai hatsari" Okonjo Nweala tace Duke ya shawarce ta da kada tayi aiki karkashin shugabancin Goodluck Jonathan a 2011,ta kara da cewa niyyar Duke shine ya hana Gwamnatin Jonathan aikin da ya dace don ta kasa nasara.

A shafin Duke na tweeter ya rubuta "Da gaske ne na hadi da Ngozi lokacin da ake rade radin za a bata mukami.

A matsayin abokan juna, na dai gargade ta ne domin an taba korar ta a matsayin ministan kudi. Ban fadi cewa inason inganta ko nakasa Gwamnatin wani ba. Hira ce kawai ta abokantaka kuma a nan ta kare.

Daga baya kuma ta zabi ra'ayin ta wanda na girmama hakan. Amma gaskiya naga karantarta da har take yada wannan hirar. Ngozi ta bani kunya a matsayin ta na ministan kudi da tattalin arziki, duk da kudin shiga masu yawa da take karba, sai da ta kara talauta kasar fiye da yanda ta same ta."

DUBA WANNAN: Tsakanin Daurawa da diyar gwamna da 'yan hakika a Kano

A kwanakin baya dai Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa : a daren lahadi, 14 ga watan janairu a Abuja, Donald Duke yace zai yi takarar shugabancin kasar Najeriya a zaben 2019.

Yace "Hakkina ne inyi shugabancin kasar nan. Hakkina ne. Ta hanyar da ta dace zan nema. Bana gujewa nauyin da ya hau kaina. Ina da abinda ake bukata na shugabancin kasar nan."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel