Kishin-kishin: Shugaba Buhari ya fadawa Gwamnoni su zabi Oshiomole a maimakon Oyegun

Kishin-kishin: Shugaba Buhari ya fadawa Gwamnoni su zabi Oshiomole a maimakon Oyegun

- Jiya ne Shugaba Buhari ya gana da Gwamnonin APC cikin dare

- Shugaban kasar ya nemi a marawa Adams Oshimole baya a zabe

- Zai yi wahala kenan Oyegun ya iya komawa kan kujerar sa a haka

Mun samu labarin yadda taron da aka yi da Buhari da kuma Gwamnonin Jam’iyyar sa ta APC a jiya ta kaya. Yanzu haka mun ji kishin-kishin din cewa Shugaba Buhari ya zauna da Gwamnonin ne kan zaben da aka shirya na Jam’iyya.

Kishin-kishin: Shugaba Buhari ya fadawa Gwamnoni su zabi Oshiomole a maimakon Oyegun

Wanene na zaba tsakanin Oyegun da Oshiomole a APC?

Idan ba ku manta ba a jiya Shugaba Buahri ya gana da Gwamnonin APC cikin dare daga karfe 8:30 har kusan 11:00. Shugaban kasar ya nemi Gwamnoni su marawa Adams Oshiomole baya a matsayin Shugaban Jam’iyyar na APC.

KU KARANTA:

Wata Majiya daga Jaridar New Telegraph ta bayyana mana wannan labari. Shugaba Buhari ya bada goyon bayan sa ne ga tsohon Gwamnan Edo Adams Oshiomole a maimakon Shugaban Jam’iyyar wanda ke kai yanzu John Oyegun.

Sai dai ba a sani ba ko John Oyegun zai nemi ya sake takara ganin inda Shugaban kasa Buhari ya karkata. Dama jiya Legit.ng ta rahoto maku cewa Gwamnan Jihar Edo Mista Godswin Obaseki ya nuna goyon bayan sa ga Adams Oshiomole.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel