Saura kiris: An nemi a kuma tada wani bam a cikin Garin Bama

Saura kiris: An nemi a kuma tada wani bam a cikin Garin Bama

- Wasu ‘yan kunar bakin-wake sun nemi su tada bam a Bama

- Kwanan nan ne dai mutanen Bama su ka tare a garin na su

- Ko a kwanaki an tada wani bam da ya kashe jama’a a Garin

Dazu mu ka ji cewa Jami’an tsaro sun gano cewa an shirya tada wani bam a Garin Bama da ke Borno. ‘Yan Boko Haram na neman sun fitini mutanen Bama da su ka tare kwanan nan bayan tsawon lokaci su na sansani gudun hijira.

Saura kiris: An nemi a kuma tada wani bam a cikin Garin Bama

Bam a bama: An fitini mutane daga dawowan su gida

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta bakin ‘Yan jarida sun bayyyana cewa sun kawar da wani bam da aka yi yunkurin tadawa a cikin Garin Bama. DSP Edet Okon ne ya bayyana wannan a jiya Talata inda yace saura kiris ayi barna.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai kai ziyara Jihar Bauchi yau

Babban Jami’in ‘Yan Sandan yake cewa wasu ‘yan kunar bakin wake har 3 sun yi kokarin yin abin da su ka saba a Yankin Ajilari da ke cikin Garin Bama. Allah dai ya sa an dace Jami’an tsaro sun ankara da su cikin gaggawa.

‘Yan kunar bakin waken sun tada bam din ba kamar yadda su ka shirya ba wanda hakan ya sa su ka kashe kan su ba tare da taba kowa. Idan ba ku manta ba Legit.ng ta rahoto cewa ban ta kashe mutane a Garin Bama kwanan nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel