Jama’an jihar Bauchi sun kammala shirin tarbar Buhari a ranar Alhamis

Jama’an jihar Bauchi sun kammala shirin tarbar Buhari a ranar Alhamis

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Bauchin Yakubu a ranar Alhamis 26 ga watan Afrilu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan watsa labaru na jihar Bauchi, Alhaji Umar Sade ne ya sanar da haka a ranar Talata 24 ga watan Afrilu, inda yace Buhari zai kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin jihar ta kammala a garin Misau, da kuma karamar hukumar Katagum.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bayyana alhininsa game da harin da yan bindiga suka kai Coci

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan yana fadin shugaba Buhari zai kaddamar da raba motocin tarakta guda 500 ga manoman jihar, inda ya tabbatar da cewar a yanzu shirye shirye ya kammala don ganin an baiwa shugaban kyakkyawar tarba.

Jama’an jihar Bauchi sun kammala shirin tarbar Buhari a ranar Alhamis

Buhari

Kwamishinan yayi kira ga jama’an Bauchi da su fito kwansu da kwar kwata su tarbi Buhari, musamman ganin cewa jihar Bauchi na daga cikin jihohin da shugaba Buhari ke da masoya na hakika.

Da majiyar mu ta zagaya jihar ta hangi fastoci da hotunan shugaban kasa Buhari da na gwamnan jihar, Muhammed Abubakar sun mamaye birnin jihar, yayin da aka kawata shatale tale da kalaman maraba ga shugaban kasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel