Gwamnonin jam’iyyar APC sun sanya labule da shugaba Buhari a fadar Villa

Gwamnonin jam’iyyar APC sun sanya labule da shugaba Buhari a fadar Villa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakoncin Gwamnonin APC

- Gwamnonin jam'iyyar APC sun bayyana ma Buhari matsayinsu game da shugaban jam'iyyar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakoncin gwamnonin jam’iyyar APC a fadar gwamnatin tarayya dake babban birnin tarayya Abuja, Aso Rock Villa, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bayyana alhininsa game da harin da yan bindiga suka kai Coci

Gwamnonin jam’iyyar APC sun sanya labule da shugaba Buhari a fadar Villa

Taron

Ganawar ta wakana ne a ranar 24 ga watan Afrilu, inda rahotanni suka bayyana cewar shuwagabannin na jam’iyyar APC sun tattauna ne kan al’amuran da suka shafi Najeriya, da kuma matsayin shugaban jam’iyyar, John Oyegun.

Daga cikin gwamnonin akwai shugaban gwamnonin jam’iyyar APC, Rochas Okorocha, shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Abdul Aziz Yari, shugaban gwamnonin Arewa, Kashim Shettima.

Gwamnonin jam’iyyar APC sun sanya labule da shugaba Buhari a fadar Villa

Taron

Sauran gwamnonin da suka halarci taron sun hada da gwamnonin jihohin Kano, Katsina, Ogun, Oyo, Filato, Nassarawa, Kano, Kogi, Edo, Adamawa, Neja da kuma mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

Gwamnonin jam’iyyar APC sun sanya labule da shugaba Buhari a fadar Villa

Trapn

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel