Shugaba Buhari ya bayyana alhininsa game da harin da yan bindiga suka kai Coci

Shugaba Buhari ya bayyana alhininsa game da harin da yan bindiga suka kai Coci

- Buhari ya jajanta ma mabiya addinin Kirista bisa kashe kashen yan bindiga a Benuwe

- Buhari yayi alkawarin gwamnati za ta kamo duk masu hannu cikin harin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da sakon ta’aziyya ga gwamnatin jihar Benuwe, al’ummar jihar, jama’an kauyen Mbalom tare da manyan Limamai da Fastocin Cocin St.Ignatius, bisa harin kisan kiyashi da yan bindiga suka kai Cocin a ranar Talata 24 ga watan Afrilu.

“Idan ba shaidan ba, babu wanda zai afka ma mutane a wajen bautansu babu gaira babu dalili, daga ganin wannan harin ka san da gangan aka shirya shi da nufin gwara kan mabiya addinai don kunna rikici a tsakaninsu.

KU KARANTA: Jami’an Yansanda sun cafke wani kasurgumin Dan fashi da makami, da makamai rututu

“Ina tabbatar ma jama’an Benuwe, da ma sauran yan Najeriya cewa zamu kamo duk wadanda suka kai harin nan, da ma sauran masu hannu cikin hare haren, kuma zamu tabbatar an bi ma wadanda harin ya shafa hakkinsu.” Inji shugaban kasa Muhmmadu Buhari.

A ranar Talata ne yan bindiga suka kai wani mummunan hari, inda suka kashe mutane goma sha biyar, 15, tare da manyan limamai guda biyu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel