Laftanar janar Buratai ya kaddamar da wani katafaren gini don amfanin Sojojin Najeriya

Laftanar janar Buratai ya kaddamar da wani katafaren gini don amfanin Sojojin Najeriya

Babban hafsan Sojan kas,a laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ya kaddamar da wani katafaren gini a kwalejin horas da manyan hafsoshin soji a barikin WU Bassey dake babban birnin tarayya Abuja.

Legit.ng ta ruwaito wannan katafaren ginin da rundunar mayakan soji ta gina don amfanin manyan hafsoshin Soji an kammala shi ne cikin watanni hudu kacal.

KU KARANTA: Jami’an Yansanda sun cafke wani kasurgumin Dan fashi da makami, da makamai rututu

A yayin jawabinsa, Buratai ya bayyana cewa an samar da kwalejin ne domin horas da hafsoshin Soja ta wajen kwarewa da sanin makaman aiki, ya kara da cewa kwalejin ta zamto babbar cibiya a nahiyar Afirka dake horas da hafsoshin Soji kan sabbin dabarun yaki da matsalolin tsaro.

Buratai yace: “A shirye muke mu fuskanci kalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta, musamman duba da sauye sauye da ake samu na zamani, don haka ya zama wajibi Sojoji su samar da sabbin dabaru magance matsalolin tsaro. Ina ja kunnen jami’an Soji da su guji shiga harkokin siyasa, kuma ba zamu lamunci siyasantar da aikin Soji ba.”

A nasa bayanin, shugaban kwalejin, Manjo janar John Enenche ya jinjin ma kokarin da Buratai ke yi wajen cigaban cibiyari, inda yace sabon katafaren ginin ya kunshi ofisoshi 29, dakunan bincike 9, dakin karatu, manyan dakunan taro, dakunan kwana duk a hawa guda uku.

Daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban askarawan Najeriya, Janar Abayomi Olanisakin, shuwagabanin SOjojin sama da ruwa, Sufetan Yansanda, shugaban DSS, Kungiyar matan hafsoshin Sojin kasa da sauransu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel