Ka-ce-na-ce da aka yi da Sanata Dino Melaya bayan zuwan sa Majalisa

Ka-ce-na-ce da aka yi da Sanata Dino Melaya bayan zuwan sa Majalisa

Mun kawo maku rikicin da aka rika yi da ‘Dan Majalisar Yammacin Jihar Kogi Sanata Dino Melaya daga 2015 zuwa yanzu bayan dawowar sa Majalisa. Sanatan ba bako bane kuma yayi kaurin suna wajen abin hayaniya.

Ka-ce-na-ce da aka yi da Sanata Dino Melaya bayan zuwan sa Majalisa

An saba rikici da Sanata Dino Melaya tun kafin ya koma Majalisa

1. Yunkurin kisan-kai

Fitaccen ‘Dan Majalisar yayi ikirarin cewa Gwamna Yahaya Bello da mutanen sa sun yi kokarin kashe sa a bara. Wannan magana dai ta je ta dawo har aka ba Sanatan laifi duk da gargadin da Majalisar Dattawan kasar tayi.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun yi ram da 'Yan uwan Dino Melaye

2. Karbe kujerar sa

Sanata Dino Melaya ya gamu da barazana na kokarin yi masa kiranye daga gida, ‘Dan Majalisar yayi ta buga shari’a da Hukumar zabe wanda dai yanzu an dawo da maganar za a fara shirin yi masa kiranye daga Majalisar Dattawan.

3. Rikici da ‘Yan Sanda

Kwanakin baya Jami’an ‘Yan Sanda su kace ana neman Sanatan, sai dai wannan makon ne aka uo ram da shi a filin jirgi. Bayan Jami’an shige-da-fice sun sake shi ne kuma ‘Yan Sanda su ka damke shi a Ranar Talata.

4. Takkadamar satifiket

An yi ta rikici da Sanatan kan abin da ya nemi ya zama badakala game da takardar shaidar sa. Sai da ta kai dai Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ta wanke ‘Dan Majalisar

Bayan nan ‘Dan Majalisan yayi rikici da irin su Shugaban Hukumar kwastam Hameed Ali da Shugaban Hukumar EFCC kan wasu bincike da ake yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel