Sun mana nisa: Dubi kudaden da gwamnatin Legas ta tara a wannan shekarar kadai

Sun mana nisa: Dubi kudaden da gwamnatin Legas ta tara a wannan shekarar kadai

- Gwamnatin legas:Tayi bajintar samar da kudaden shiga da yawan su yakai biliyan N141.96 a Q1 2018

- Jihohi da ywa basu iya dogaro da kansu sai ta Tarayya ta agaza musu

- Jihar Legas tafi kowacce jiha arziki, don da babban birni ce kuma tanna gabar ruwa

Sun mana nisa: Dubi kudaden da gwamnatin Legas ta tara a wannan shekarar kadai

Sun mana nisa: Dubi kudaden da gwamnatin Legas ta tara a wannan shekarar kadai

Kwamishinan kasafin kudi da kuma tsara tattalin arziki na jahar legas Mr Olusegun Banjo ya bayyana a ranar Talata nan cewa sun tara kudaden shiga wanda yawansu yakai biliyan N141.96 a cikin kwatan shekarar nan ta 2018.

Banjo yace wannan shine abinda yake guda na a kasar a jawabin na sanya alama akan gwamnatin Akinwunmi Ambode a shekarar sa ta uku a Ofis Alausa jahar legas.

Banjo ya kara da cewa adadin ya bayyana karin kashi 60 da aka samu akan Biliyan 124.14 da aka samu a shekara ta 2017.

A bangaren sa yace kasafin kudin ya karu da biliyan 17.82 akan na shekara ta 2017.

Banjo yace hukumar kula da shige da ficen kudade (LIRS) legas ta hada biliyan N84.19 a cikin kwatan shekarar nan ta 2018 wanda ya lisafta da kashi 80 na TIRG wanda ya ninka na shekarar 2017 da kashi 56.

Kwamishinan ya Kara da cewa jahar ta samu kudi nata na kanta wanda yakai biliyan N24.96 wanda ya haura na shekara ta 2017 wanda hakan yayi nuni da haurawar sa da kashi 88.

DUBA WANNAN: Yawan yaran da aka ceto daga almajirta a jihar Kano ya zuwa yanzu

Yace wannan wata manuniya ce dake nuni da cewa an kusa cimma manufa duk da cewa akwai abubuwa da dama da zasuyi.

A yayin duba wani aiki da kuma kimantawa kwamishinan yace hukumar ba zata maida hankali wajen kula da ayyukan gwamnati kawai ba har sai an samu ci gaban daya kamata a jahar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel