Kotu ta bayar da umarni ga hukumar EFCC na garkame tsohon gwamnan jihar Katsina, Shema

Kotu ta bayar da umarni ga hukumar EFCC na garkame tsohon gwamnan jihar Katsina, Shema

A halin yanzu dai tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema, yana garkame a wurin hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC har zuwa ranar 27 ga watan Afrilu.

Kotu ta bayar da umarni ga hukumar EFCC na garkame tsohon gwamnan jihar Katsina, Shema

Kotu ta bayar da umarni ga hukumar EFCC na garkame tsohon gwamnan jihar Katsina, Shema

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, babbar kotun tarayya ta jihar Katsina dake gudanar da shari'ar tsohon gwamnan ba ta kama shi da laifin zambar kudi na sama da Naira Biliyan biyar da hukumar EFCC ke tuhumar sa da aikatawa ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar ta EFCC dai tana zargin tsohon gwamnan da wawushe N5,776,552,396 na kudin tallafi na SURE-P (Subsidy Re-investment and Empowerment Programme) a yayin da yake rike da kujerar gwamnatin jihar sa.

Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar EFCC tana zargin tsohon gwamnan da aikata laifin a tsakanin watan Yunin 2014 da kuma Mayun 2015 inda suka yi tarayya da wani Idris Kwado wajen almundahanar da ta sabawa sashen na 18 cikin dokokin kiyaye tattalin arziki.

KARANTA KUMA: Al'amurran tsaro 5 da suka bukaci Shugaba Buhari ya kawo ƙarshen su a Najeriya

Baya ga wannan tuni dai daman Shema da wasu mutane uku na fuskantar shari'a a gaban babbar kotun jihar sa bisa zargi na aikata laifin almundahana ta Naira biliyan 11 wanda shima hukumar EFCC ke tuhumarsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel