Wasikar Buhari ta jawo barkewar cece-kuce da rabuwar kayuwa a tsakanin 'yan majalisar wakilai

Wasikar Buhari ta jawo barkewar cece-kuce da rabuwar kayuwa a tsakanin 'yan majalisar wakilai

Wasikar da Buhari ta jawo barkewar cece-kuce da rabuwar kayuwa a zaman majalisar wakilai na yau.

Wasu 'yan majalisar wakilan Najeriya sun bayyana biyan fiye dalar Amurka miliyan 400 domin sayen wasu jiragen yaki da cewar ya saba ka'ida kuma laifi ne da kan iya kai wa ga tsige shugaban kasa.

'Yan majalisar sun bayyana hakan ne bayan karanta wasikar da shugaba Buhari ya aike wa majalisar kuma aka karanta a zauren majalisar yayin zaman ta na yau.

Wasikar Buhari ta jawo barkewar cece-kuce da rabuwar kayuwa a tsakanin 'yan majalisar wakilai

Wasikar Buhari ta jawo barkewar cece-kuce da rabuwar kayuwa a tsakanin 'yan majalisar wakilai

A cikin wasikar, shugaba Buhari, ya bayyana cewar, an fitar da kudin ne bisa tsammanin majalisar zata zartar da kasafin kudin bana a kan lokaci.

Buhari ya bayyana cewar an kulla cinikin jiragen ne tsakanin gwamnatin Najeriya da ta Amurka saboda karancin lokacin da kasar Amurka ta bayar na cinikin.

DUBA WANNAN: Bayan ganawar sirri da Buhari, Alkalin alkalan Najeriya ya ce alkalai basu da laifi

Duk da majalisar bata fara mahawara a kan wasikar ba, wasu mambobin majalisar sun ce wasikar tamkara manuniya ce ga karen tsaye da Buhari ya yiwa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Tuni dai majalisar dattijai ta aikewa Ministar kudi, Kemi Adeosun, da Ministan tsaro, Mansur Dan-Ali, da gwamnan babban banki, Godwin Emefiele, sammacin su bayyana a gaban ta domin kare kan su dangane da batun sayen jiragen bayan Sanata Samuel Anyanwu, ya jawo hankalin majalisar a kan batun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel