Shugaba Buhari zai ziyarci jihar Bauchi a ranar Alhamis

Shugaba Buhari zai ziyarci jihar Bauchi a ranar Alhamis

Rahotanni da sanadin shafin jaridar Daily Trust sun bayyana cewa, ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar kwana guda jihar Bauchi a ranar Alhamis 26 ga watan Afrilu.

Jaridar ta ruwaito wannan rahoto ne da sanadin Kwamishinan yada labarai da al'adu na jihar, Umar Ibrahim Sade da ya bayyana a yayin ganawa da manema labarai.

A cewar sa, ana sa ran shugaban kasar zai kaddamar da wasu sabbin aikace-aikace na malala tituna a birnin jihar da kuma wasu sassa na kananan hukumomin Misau da Katagum wanda gwamnatin jihar ta gudanar.

Shugaba Buhari zai ziyarci jihar Bauchi a ranar Alhamis

Shugaba Buhari zai ziyarci jihar Bauchi a ranar Alhamis

Shugaban kasar zai kuma kaddamar da raba manyan motoci 500 na aikin gona ga manoma bisa yarjejeniya ta bashi da gwamnatin jihar ta kulla da wani kamfani mai zaman kansa.

KARANTA KUMA: Matasa Kadara ce mai Muhimmiyar Daraja ga kowace Kasa - Jakadan UN

Legit.ng ta fahimci cewa, tuni Kwamishinan ya kirayi al'ummar jihar akan fitowa wajen tarbar shugaban kasa da kuma karrama shi domin tabbatar da nasarar wannan ziyara.

A yayin haka tuni dai an fara gudanar da shirye-shirye na maraba da shugaba Buhari yayin da fastocin sa da na gwamnan jihar Muhammad Abubakar suka mamaye manyan hanyoyi na cikin birnin jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel