Za a kara tsaro a cikin Majalisar Tarayyar Najeriya Inji Bukola Saraki

Za a kara tsaro a cikin Majalisar Tarayyar Najeriya Inji Bukola Saraki

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya bayyana cewa za su dauki matakin da zai taimaka wajen kara inganta tsaro a Majalisar kasar bayan abin da ya faru kwanan nan.

A makon jiya dai idan ba ku manta ba wasu tsageru sun shiga har cikiin Majalisat Dattawa inda su kayi gaba da sandar girman da aka ajiye. Saraki a lokacin ya tafi wani taro game da tattalin arzikin Duniya da aka shirya a kasar Amurka.

Za a kara tsaro a cikin Majalisar Tarayyar Najeriya Inji Bukola Saraki

Bukola Saraki yace za a kara tsaro a Majalisar Tarayya

Bukola Saraki ya bayyana cewa zai kafa wani kwamitin hadaka tsakanin ‘Yan Majalisar Dattawa da kuma Takwararorin su na Majalisar Wakilai da zai bincike abin da ya faru kwanaki sannan kuma su kawo matakin da ya kamata a bi.

KU KARANTA: An yi gigin tunbuke Shugaba Buhari a Majalisar Tarayya

A makon na yake bayyana cewa za ayi wannan ne domin ganin babu wanda ya kara fin karfin Jami’an tsaron da ke aiki a Majalisun kasar. Saraki yace a su hada kai da sauran Hukumomi da 'Yan Sanda domin ganin an magance matsalar.

An dai yabawa kokarin da Majalisar tayi lokacin da wannan mummunan abu ya faru. Dalilin haka ne Bukola Saraki ya zauna da Takwaran sa Yakubu Dogara. Dama can kun ji cewa Jami’an tsaro na SARS sun yi gaba da ‘Dino Melaye zuwa Lokoja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel