Babban ci gaba: A bara dala biliyan 22 'yan Najeriya masu zama kasar waje suka aiko gida

Babban ci gaba: A bara dala biliyan 22 'yan Najeriya masu zama kasar waje suka aiko gida

- Tattalin arzikin Najeriya na kara farfadowa sannu a hankali

- Kudaden zuba jari da na hada-hada suna habaka a cikin gida

- Masu aiki a kasar waje sun turo kudi gida

Babban ci gaba: A bara dala biliyan 22 'yan Najeriya masu zama kasar waje suka aiko gida

Babban ci gaba: A bara dala biliyan 22 'yan Najeriya masu zama kasar waje suka aiko gida

Babban bankin duniya ya bayyana cewar kudin da 'yan Najeriya mazauna kasashen waje suke turo wa gida ya kai dala biliyan 22 a shekarar 2017, inda suka zama na biyar a duniya na masu tura kudi zuwa kasashen su, sannan kuma suka zama na daya a nahiyar Africa.

Har ila yau Bankin Duniyan ya bayyana cewar farashin canja kudi wanda ake tura wa zuwa wasu kasashen ya karu.

Majiyar mu Legit.ng ta samu rahoton cewa bankin duniya ya bayyana cewar an samu karin kudin da ake aikawa zuwa wasu kasashen ne ta dalilin yawan da bakin haure suka yi a yankin Turai, Russia da kuma kasar Amurka.

A shekarar 2017 masana sun tabbatar da cewar an samu rahoton samun dala biliyan 466 an samu karin kusan kashi 8 da digo 5 cikin dari akan na shekarar 2016, inda aka samu dala biliyan 429, a cewar bankin.

Sannan kuma ana saka ran za'a kara samun karuwar shigar kudaden da kaso 4 cikin dari a shekarar 2018. Kasashen da suka fi karbar kudaden sune; Indiya dala biliyan 69, China dala biliyan 64, Philippines dala biliyan 33, da kuma kasar Mexico da dala biliyan 31.

DUBA WANNAN: Ashe kudin 'ajiyar Abacha sun hayayyafa

A nahiyar Afrika kuma kasar Najeriya da kasar Masar ne suka take musu baya. Masana sun bayyana cewar; yayin da aka samu karin kudaden a wasu kasashen na duniya, wasu makarantu, cibiyoyi da hukumomi zasu yi sauki, saboda kara samun hanyar shigar kudin ga iyalan masu kudaden.

A dalilin haka babban bankin duniya yayi kira ga kasashen dasu dauki matakai don saukaka tsarin, ciki kuwa har da shigar da tsarin fasaha.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel