Sai da shugaba Buhari yayi gaban kansa kan wasu miliyoyin daloli sannan ya gaya wa 'yan majalisar tarayya

Sai da shugaba Buhari yayi gaban kansa kan wasu miliyoyin daloli sannan ya gaya wa 'yan majalisar tarayya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar wakilai da su saka bayanin sayen jiragen yaki na (Super Tucano Aircraft) a kasafin kudin bana, duk da ya fitar da kudin ba tare da sahalewarsu ba a bara, zagaye da ka iya jawo wa a tsige shi in sun so.

Sai da shugaba Buhari yayi gaban kansa kan wasu miliyoyin daloli sannan ya gaya wa 'yan majalisar tarayya
Sai da shugaba Buhari yayi gaban kansa kan wasu miliyoyin daloli sannan ya gaya wa 'yan majalisar tarayya

A cikin wata wasika da shugaban majalisar wakilan ya karanta, Honorable Yakubu Dogara, Buhari yace ya bada izinin fitar da kudaden ne saboda yasan cewar majalisar wakilan zata goya masa baya.

"Na bada izinin fitar da kudin ne saboda na tabbata majalisar wakilan baza tayi watsi da kudurin nawa ba na sayen wadannan jiragen saman na musamman, wadanda zasu kawo cigaba sosai a harkar tsaro a kasar nan, na bada izinin a cire dala 469,374,470.00 a cikin asusun rarar man fetur na kasar nan," inji Buhari.

Kudin dai an fitar dasu ne domin yaki da ta'addanci a kasar nan, hakan ya biyo bayan ya bada izinin cire dala miliyan 462 daga asusun rarar kudin man fetur domin a biya kudin jiragen.

Shugaban kasar ya aika da wasikar zuwa ga shugaban majalisar wakilan a ranar 13 ga watan Afrilun nan, inda shi kuma shugaban majalisar wakilan ya karbi wasikar a ranar 17 ga watan Afrilun.

Wasikar ta nuna cewar shugaban kasar ya riga ya bada izinin sayo jiragen, kawai yana son majalisar wakilan ta saka bayanin ne a cikin kasafin kudin wannan shekarar ne da majalisar har yau take aiki akai.

Idan ba a manta ba majiyar mu Legit.ng ta ruwaito cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada izinin cire dala miliyan 462 daga asusun rarar kudin danyen mai, don sayo jiragen daga kasar Amurka, inda yayi hakan ba tare da amincewar majalisar dokoki ba.

Da yake jawabi Kingsley Chinda (PDP Rivers) ya kawo dokar kundin tsarin mulki, na sashi 80 da 81, inda yayi magana akan fitar da kudi ba tare da saka hannun majalisar dokoki ba.

Ya ce dokar Najeriya bata amince da wannan matakin da shugaban kasar ya dauka ba. Idan muka ki yarda da kudurin nashi menene zai faru? inji shi. Ya kara da cewar hakan dama yasha faruwa a gwamnatin Buharin, inda ya bukaci da a tsige shugaban kasar.

DUBA WANNAN: Ashe ajiyar Abacha a Turai ta hayayyafa

Sunday Karimi (PDP, Kogi) daya daga cikin 'yan majalisar wakilan shima ya nuna rashin amincewar shi, inda ya bayyana kudurin shugaban kasar a matsayin nuna isa.

"Tunda har ya fito ta wannan hanyar domin ya tursasa mu mu yarda da kudurin shi ya kamata shima ya jira mai zai biyo baya."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel