Jami’an Yansanda sun cafke wani kasurgumin Dan fashi da makami, da makamai rututu

Jami’an Yansanda sun cafke wani kasurgumin Dan fashi da makami, da makamai rututu

Rundunar Yansandan Najeriya, reshen jihar Bayelsa ta yi caraf da wani gagararren dan fashi da makami a garin Yenagoa, sa’annan sun gano muggan makamai da suka hada da bindigu da harsasai.

Kaakakin rundunar Yansandan DSP Asinin Bustwat ya bayyana ma majiyar Legit.ng cewa jami’an Yansandan SARS ne suka kama kasurgumin Dan fashi a garin Ovom, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

KU KARANTA: Yan bindiga sun bindige manyan Fastoci 2, masu bauta guda 15 a Cocin jihar Benuwe

“Bayan binciken kwakaf a gidansa, Jami’an SARS sun gano karamar Bindiga mai lamba PK401158 tare da alburusai, haka zalika sun gano wata karamar bindigar toka, wayoyi kirar Infinix da Techno, adduna, tabar wiwi da na’urar kwamfuta kirar Toshiba.” Inji Bustwat.

Kaakaki Bustwat ya bayyana cew zasu cigaba da farautar sauran yan gungun fashin da makamin don gurfanar dasu gaban kuliya manta sabo inji rahoton majiyar Legit.ng.

Daga karshe Kaakakin tabbatar da manufar rundunar Yansandan jihar don tabbatar da zaman lafiya tare da kare dukiyoyi da rayukan al’umma na jihar daga ayyukan matsafa da yan fashi da makami.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel