Majalisa ta kafa kungiya ta musamman sakamakon harinda aka kai mata

Majalisa ta kafa kungiya ta musamman sakamakon harinda aka kai mata

- Bayan zaman awowi uku, majalisa ta kafa wata kungiya ta musamman wadda zata kara tabbatar da tsaro a majalisar

- Jami’in labarai ya bayar da rahoton cewa an fara zaman ne da karfe 10.56 na safe, aka gama da karfe 1.36 na rana

Bayan zaman awowi uku, majalisa ta kafa wata kungiya ta musamman wadda zata kara tabbatar da tsaro a majalisar.

Jami’in labarai ya bayar da rahoton cewa an fara zaman ne da karfe 10.56 na safe, aka gama da karfe 1.36 na rana.

Shugaban majalisar Bukola Saraki lokacin da yake jawabi bayan gama taron, yace kungiyar zata hada mambobin majalisun biyu, ta dattijai data wakilai.

Majalisa ta kafa kungiya ta musamman sakamakon harinda aka kai mata

Majalisa ta kafa kungiya ta musamman sakamakon harinda aka kai mata

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa Shuwagabannin majalisa sun gudanar da taro game Satar Sandar Girma, a harin da wasu ‘yan ta’adda suka kai a majalisar a ranar Laraba data gabata.

KU KARANTA KUMA: Wani matashi yayi amfani da alewa yaja hankalin yarinya ‘yar shekara 6 ya mata fyade a cikin bandaki

Duk da cewa ba’a bar manema labarai sun shiga wurin taron ba, amma daya daga cikin ma’aikatan Saraki ya bayyana cewa sun gudanar da taron ne game satar Sandar Girma ta majalisa da kuma lamarin Sanatoci magoya bayan shugaba Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel