Wadansu da aka ceto daga Libya suna zanga-zanga, ji dalilansu masu ban dariya

Wadansu da aka ceto daga Libya suna zanga-zanga, ji dalilansu masu ban dariya

- Banki na cire musu N1,050 daga cikin kudinsu na ceto, shine babbar matsalarsu

- Har sun mantada bakar azabar da suka sha a Libya

- Jihar Edo tafi kowa yawan masu gudun hijira zuwa Italiya a Najeriya

Wadansu da aka ceto daga Libya suna zanga-zanga, ji dalilansu masu ban dariya

Wadansu da aka ceto daga Libya suna zanga-zanga, ji dalilansu masu ban dariya

A yau dinnan ne wasu daga cikin mutanen da aka dawo da su daga kasar Libya, suka hada zanga-zangar lumana a gidan gwamnatin jihar Edo dake Benin City, don nuna rashin amincewar su akan kudaden da bankuna suke daukar musu kowanne wata, inda da yawa daga cikin su suka ce asusun nasu basa yin aiki.

An gabatar da zanga zangar ne cikin lumana, inda suka gabatar da matsalolin su da suka hada da kudin da banki yake dauka kimanin Naira 1,100 a matsayin kudin kula da katin ATM da dai sauran su. Bayan sun kammala zanga zangar, sun aika da budaddiyar wasika ga gwamnan jihar ta Edo, Godwin Obaseki, inda jami'an gwamnatin jihar suka karbi wasikar don mika ta ga gwamnan.

DUBA WANNAN: Farfesa mai fesarwa ya gamu da gamonsa

A baya majiyar mu Legit.ng ta taba rawaito cewa a lokacin da 'yan Najeriyan suka dawo daga kasar ta Libya, Gwamna Obaseki ya amince da a basu wuri mai girman Hectares 150 da kuma kudi naira miliyan 100 domin suyi noma.

Gwamnatin jihar ta bada kudaden ga wadanda suka gama makarantar koyan sana'o'i ta Edo Agricultural Development Programme, wadanda ta ke da ofis a babban birnin jihar na Benin City.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel