Almajirta: Yara 26,000 muka ceto a bana - Daurawa, Shaihun Hisba

Almajirta: Yara 26,000 muka ceto a bana - Daurawa, Shaihun Hisba

- Akwai almajirai miliyan ukku a jihar Kano, kuma iyayensu yawanci ba Kanawa bane

- An tsinci 26,000 suna gararmba cikin shekaru biyu a jhar Kano

- Almajirta dai bata da wani alffanu ga 'ya'yan Arewa, kuma babu dalilin bautar da yaro

Almajirta: Yara 20,000 muka ceto a bana - Daurawa, Shaihun Hisba

Almajirta: Yara 20,000 muka ceto a bana - Daurawa, Shaihun Hisba

Shugaban hukumar hisba ta jihar Kano, mai kokarin tsayar da shari'ar Islama, Dr. Aminu Daurawa, yace a shekaru biyu da suka wuce, akalla almajirai 26,000 suka ceta daga bara da wahalar birni, suka mayar dasu kauyukansu.

A cewarsa, dukkan yaran yawancin su basu da wani isasshen hankalin kula da kansu ko ciyar da kansu, amma iyayensu suka wullo su bara.

Ana sa rai akalla akwai almajirai 3m a Kano, 12,000,000 a fadin Najeriya, wadanda iyayensu suka yi barbarsu amma basu iya kula da rayuwarsu ba, sai dai wayon cewa wai karatun allo suka tura su.

DUBA WANNAN: Zazzabin cizon sauro ya gagari Najeriya

Shugaban Hisbar, ya kira iyaye dasu kula da nauyin da suka dora wa kansu tunda har suka iya haifo yaran da dole ne su kula da ciyarwarsu da tarbiyyarsu.

Har yanzu dai kamar sghuwagabannin siyasa basu ma ankare da irin bala'in da yaran kan fada ba, ko kuma wanda zaman banza da girma ba ilimi zai haifar a nan gaba.

Almajirta dai ita ta haifar da Boko Haram a yau, ta haifar da Maitsatsine, a baya kuma ta kawo jihadin dan-Fodio wanda ya karade adin yankin Najeriya da jihadi da bautarwa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel