Wani matashi yayi amfani da alewa yaja hankalin yarinya ‘yar shekara 6 ya mata fyade a cikin bandaki

Wani matashi yayi amfani da alewa yaja hankalin yarinya ‘yar shekara 6 ya mata fyade a cikin bandaki

- Kotun Ikeja ta tura wani tashi zuwa gidan horon yara bisa ga laifin yiwa yarin ‘yar shekara 6 fyade a cikin ban daki

- Alkaliyar kotun Mrs B.O Osunsanmi, wadda ta yanke hukuncin tace matashin dan shekara 16 a cigaba da ajiyeshi har zuwa lokacin da Daraktan jiha na gabatar da kara (DPP) zai shawarci a sakeshi

- ASP Ezekiel Ayorinde mai gabatar da kara ya bayyanawa kotu cewa matashin ya sanya yatsunsa a gaban yarinyar

Kotun Ikeja ta tura wani tashi zuwa gidan horon yara bisa ga laifin yiwa yarin ‘yar shekara 6 fyade a cikin ban daki.

Alkaliyar kotun Mrs B.O Osunsanmi, wadda ta yanke hukuncin tace matashin dan shekara 16 a cigaba da ajiyeshi har zuwa lokacin da Daraktan jiha na gabatar da kara (DPP) zai shawarci a sakeshi.

ASP Ezekiel Ayorinde mai gabatar da kara ya bayyanawa kotu cewa matashin ya sanya yatsunsa a gaban yarinyar. Yace wanda ake zargin ya aikata laifin a ranar 17 ga watan Afirilu a unguwar Abule-Egba.

Wani matashi yayi amfani da alewa yaja hankalin yarinya ‘yar shekara 6 ya mata fyade a cikin bandaki

Wani matashi yayi amfani da alewa yaja hankalin yarinya ‘yar shekara 6 ya mata fyade a cikin bandaki
Source: Twitter

Duk da cewa matashin bai amsa laifin nasa ba, amma laifin nasa ya sabawa sashe na 134 na dokar ta’addanci ta jihar Legas, 2015.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa da babban alkalin Najeriya a Aso Rock

NAN ta ruwaito cewa sashen dokar ya yanke shekaru bakwai a gidan jarum ga wanda ya aikata irin wannan laifi. An kuma daga karar zuwa ranar 28 ga watan Mayu.

A baya Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar ‘Yan Sanda a jihar Legas ta kama wani mutum mai shekaru 50, Taiwo Oyelabi, bisa ga laifin aikata zina da diyar cikinsa wadda a yanzu take da shekaru 21 a duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel