Yan bindiga sun bindige manyan Fastoci 2, masu bauta guda 15 a Cocin jihar Benuwe

Yan bindiga sun bindige manyan Fastoci 2, masu bauta guda 15 a Cocin jihar Benuwe

Wasu yan bindiga sun kai farmaki a wani Cocin mabiya darikar Katolika, mabiya addinin Kirista, inda suka bindige mutane goma sha biyar, 15, a kauyen Aya-Mbalom, jihar Benuwe, inji rahoton Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan hari ya faru ne a karamar hukumar Gwer ta gabas, kamar yadda Kaakakin gwamnan jihar Benuwe Terver Akase ya bayyana, inda yace yan bindigan sun kona gidaje 50, suka tashi kauyen gaba daya.

KU KARANTA: Dubun yan bindigar da suka kashe Dansandan dake gadin gonar Magu ta cika

Daga cikin wadanda aka kashe akwai manyan Limaman Cocin, Joseph Gor da Felix Tyolaha. Sai dai Kwamishinan Yansandan Najeriya, Fatai Owoseni tare da Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Moses Yamu basu tabbatar da harin ba.

Yan bindiga sun bindige manyan Fastoci 2, masu bauta guda 15 a Cocin jihar Benuwe

Hare hare

Wanann hari ya faru ne kimanin kwanakin goma da kai wani mummunan hari a karamar hukumar Guma na jihar Benuwe, inda wasu yan bindiga suka bude wuta a kauyen Guma, suka kashe mutane da dama.

A wani labarin kuma, Sojojin Najeriya sun kona gidaje da dama a kauyen Naka dake cikin karamar hukumar Gwer ta gabas, bayan wani hari da matasan kauyen suka kai ma wani jami’in Soja, wanda yayi sanadiyyar mutuwarsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel