Saraki Dogara da sauransu sun hadu akan sace sandar iko

Saraki Dogara da sauransu sun hadu akan sace sandar iko

- Shuwagabannin majalisa sun gudanar da taro game Satar Sandar Girma, a harin da aka kai a majalisar a ranar Laraba data gabata

- Daya daga cikin ma’aikatan Saraki ya bayyana cewa sun gudanar da taron ne game satar Sandar Girma ta majalisa da kuma lamarin Sanatoci magoya bayan shugaba Buhari

- Babban sashen majalisar ya dakatar da sakataren kungiyar Sanatocin magoya bayan shugaba Buhari saboda ya kai majalisar kara kotu akan canja dokar zabe

Shuwagabannin majalisa sun gudanar da taro game Satar Sandar Girma, a harin da wasu ‘yan ta’adda suka kai a majalisar a ranar Laraba data gabata.

Duk da cewa ba’a bar manema labarai sun shiga wurin taron ba, amma daya daga cikin ma’aikatan Saraki ya bayyana cewa sun gudanar da taron ne game satar Sandar Girma ta majalisa da kuma lamarin Sanatoci magoya bayan shugaba Buhari.

Taron an gudanar dashi ne a gidan shugaban majalisar Bukola Saraki dake Maitama a birnin tarayya daga karfe 8 na dare zuwa karfe 11.30 na dare.

Saraki Dogara da sauransu sun hadu akan sace sandar iko

Saraki Dogara da sauransu sun hadu akan sace sandar iko
Source: Depositphotos

Majalisar ta bayyana cewa kungiyar Sanatocin wadanda ke goyon bayan shugaba Buhari game da canja dokar zabe ta 2010 a matsayin masu rauni.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa da babban alkalin Najeriya a Aso Rock

Babban sashen majalisar ya dakatar da sakataren kungiyar Sanatocin magoya bayan shugaba Buhari, Ovie Omo-Agege, saboda ya kai majalisar kara kotu akan canja dokar zabe.

Idan bazaku manta ba a makon da ya gabata ne wasu yan daba suka kai farmaki majalisar dattawan kasar inda suka arce da sandar iko na majalisar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel