Dalilan da suke kawo cikas a bangaren samar da wutar lantarki - Fashola

Dalilan da suke kawo cikas a bangaren samar da wutar lantarki - Fashola

Ministan makamashi, ayyuka da gidaje, Mr. Babatunde Fashola yace gazawa ta bangaren wuta bashi da alaka da rashin samar da fasahar zamani a kasar. Fashola ya fadi haka ne a taron karawa juna sani karo na 11 inda ya samu wakilcin babban sakatere na Ma'aikatan makamashi, ayyuka da gidaje Louis Edozein.

Yace dalilin da yasa fanin samar da wutan lantarkin ke fuskantar matsaloli bashi da alaka da rashin fasahar zamani sai dai matsalolin siyasar a fanin samar da wutan ne da kuma dokokin da suka dabaibaye fanin inda kamfanoni masu zaman kansu da na gwamnati ke tattaunawa wajen kwangilar aikin.

Dalilan da suke kawo cikas a bangaren samar da wutar lantarki - Fashola

Dalilan da suke kawo cikas a bangaren samar da wutar lantarki - Fashola

Ministan kuma ya kara da cewa Najeriya bata bayar da muhimmancin gina sauran sassan tattalin arzikin ba face man fetur kawai.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kashe wani gawurtacen 'dan ta'ada a jihar Akwa Ibom

A wajen taron babban sakatare na Petroleum Technology Development Fund Aliyu Gusau da tsohon MD na NNPC Funsho Kupolokun sunce bangaren mai da gas sunyi musu nisa sosai.

Kowa yana magana akan man fetur kullum maganar kenan amma bamuyi komai akai ba sai magana. A shekara ta 1999 a lokacin dana dawo aikin gwamnati magana daya ce kuma har yanzu ita akeyi.

Tsohon shugaban hukumar tace man fetur na kasa (NNPC) ya kara da cewa masana'antar tana fuskantar kalubale kuma hakan zaici gaba da faruwa matukar baza'a gyara ba.

Gusau yace ya yarda da cewa har yanzu mai shine a tsakiya. Matatar man fetur ce kadai keda damar samar tafiyar da tattalin arzikin. Hakan bazai samu ba matukar zamuci gaba a yanda muka dakko.

Ya kamata a dakatar da kasuwan cin dibar mai daga kasa ana cinikinsa a fadin duniya. Itace hanyar da za'abi domin samun tattalin albarkatun man fetur. Ya kara da cewa ta wannan hanyar ne zamu samu dukiya da kuma samar da ayyuka, Sannan mu samar da taki, wuta da kuma sauran sinadarai da muke bukata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel