Dalilin da yasa kasafin kudin shekarar bana ba zai samu wucewa ba yau

Dalilin da yasa kasafin kudin shekarar bana ba zai samu wucewa ba yau

Wani bincike da aka gudanar jiya Litinin ya bankado cewa, akwai yiwuwar kasafin kudin bana na Naira tiriliyan 8.6 ba zai sami wucewa ba saboda abinda 'yan majalisar dokokin suka bayyana da cewa "Cunkushewar Aiki" musamman daga kwamatin duba kasafi na majalisar.

Bincike ya nuna cewa, an sami tsaiko ne daga bangaran majalisar zartarwa da kuma majalisar dokoki wanda shine musabbabin kawo tsaiko ga kwamatin tsara kasafin na majalisar dokokin.

"Satin da ya wuce, akwai kwamatittikan da suka mika rahotan su ga kwamatin tsara kasafin kudi na majalisa. Hakan na nufin karin aiki ne sannan kuma dole a karawa kwamatin lokaci su zauna don duba rahotannin kafin su miko shi zauren majalisar ya sake dubawa" In ji wata majiya

KU KARANTA: Fusattun matasa sun halaka wani saja da ya kashe wani bako a otal

Mataimakin shugaban kwamatin, Mr. Chris Azubuogu, ya tabbata da cewa, majalisa na bukatar karin wasu ranakun kafin sa hannu a kunshin kasafin. Azubuogu ya ki bayyana adadin ranakun da majalisar ke bukata kafin sanya hannu a kasafin, ya dage kan cewa ba zai yiwu gobe (talata) ba, sai dai ko mako mai zuwa.

"Muna kan aikin duba rahotanni ne yanzu haka. Akwai sama da shafuka dubu bakwai a gaban mu. In ba'a yaba mana ba ba'a kushe mana ba. Muna bukatar karin lokaci amma gaskiya ba gobe ba" In ji mataimakin shugaban kwamatin tsara kasafin na majalisar dokoki, Chris Azubuogu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel