Yan sanda sun fesa barkonon tsohuwa ga masu zanga-zanga akan rashin dawowar yan matan Chibok 112 da suka rage a Abuja

Yan sanda sun fesa barkonon tsohuwa ga masu zanga-zanga akan rashin dawowar yan matan Chibok 112 da suka rage a Abuja

A ranar Litinin, 23 ga watan Afrilu, yan sanda sun watsa barkonon tsohuwa ga mambobin kungiyar BringBackOurGirls (BBOG) dake zanga-zanga akan rashin dawowar yan matan Chibok 112 da suka rage a Abuja.

Edith Yassin, wani mamba a kungiyar yace: “Yan sanda sun harba mana barkonon tsohuwa . bamu haura layinsu ba.

“Kawai mun tsallaka titi ne don zama a kasa kamar yadda mukeyi tun ranar 13 ga watan Afrilu lokacin da suka dauke mana kujerunmu da kuma rufe Unity Fountain. Menene dalilin da suke haramta mana fountain?

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Jami’an SARS sun sake kama Dino Melaye

“Mun gode Allah ba komai. Baya ga barkonon tsohuwar, godiyanmu yan tsirarun ababen hawa ke kan hanya lokacin da abun ya afku."

Yassin ya tabbatar da cewa babu dan kungiyar BBOG ko guda da ya ji rauni lokacin da abun ya afku.

A halin yanzu, NAIJ,com ta rahoto a baya cewa a ranar Talata, 23 ga watan Janairu, yan sanda sun kasa jagoran BBOG, tsohuwar ministar ilimi, Oby Ezekwesili da wasu mambobin kungiyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel