Kungiyar Musulmai tace Buhari ya fadi gaskiya game da matasan Najeriya

Kungiyar Musulmai tace Buhari ya fadi gaskiya game da matasan Najeriya

- Kungiyar Musulmai ta MURIC tace maganar da shugaba Buhari yayi game da matasan Najeriya

- Daraktan kungiyar Prof. Ishaq Akintola ya zargi kafar yada labarai da cewa itace ta juyawa Buhari maganarsa

- Kungiyar tace matasan tace akwai shuwagabanni da dama da sukayi irin wannan kalami game da matasan Najeriya, kamarsu Janar Babangida, Obafemi Awolowo, Atiku Abubakar, Sanata Shehu Sani, da kuma Gwamna Dickson

Kungiyar Musulmai ta MURIC tace maganar da shugaba Buhari yayi game da matasan Najeriya baiyi laifi ba, saboda sun dade suna a malalatansu.

Daraktan kungiyar Prof. Ishaq Akintola ya zargi kafar yada labarai da cewa itace ta juyawa Buhari maganarsa, saboda shugaba Buhari baiyi amfani da Kalmar malalata a cikin jawabinsa.

Kungiyar tace matasan tace akwai shuwagabanni da dama da sukayi irin wannan kalami game da matasan Najeriya, kamar su Janar Babangida, Chief Obafemi Awolowo, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Sanata Shehu Sani, da kuma Gwamna Dickson.

Kungiyar Musulmai tace Buhari ya fadi gaskiya game da matasan Najeriya

Kungiyar Musulmai tace Buhari ya fadi gaskiya game da matasan Najeriya

Idan har duk wadannan mutane da sukayi wadannan maganganu sun fito daga bangare kudu maso kudu, ga kuma tsohon shugaban kasa na mulkin Soja wanda ke daga yanki kudu maso yamma, ga kuma Sanata daga yankin arewa ai kuwa Buhari bai fadi wani sabon abu ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Jami’an SARS sun sake kama Dino Melaye

A halin da ake ciki har yanzu dai shugaba Buhari na cigaba da shan caccaka daga bangarori daban-daban akan furucin da yayi game da matasa a kasar Ingila. inda a yanzu haka wasu sun nemi ya ba matasan hakuri.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel