Najeriya na bukatar shugaban kasa Igbo - Apostle Suleman

Najeriya na bukatar shugaban kasa Igbo - Apostle Suleman

- Apostle John Suleman ya nuna goyon bayansa ga Igbo ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2019

- Suleman yace shugaban kasa Igbo mai yiwuwa ya kasance shine maganin matsalar mu a Najeriya ta fannin samar da ayyukanyi

- Yace Igbo a kasar nan sunfi kowa yawan ma’aikata da cewa kusan kowane Igbo a kasar nan yana da kasuwanci wanda ke ja

Babban limamin coci, Apostle John Suleman, ya nuna goyon bayansa ga Igbo ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2019, ya bayyan hakan ne lokacin da yake gudanar da wa’azi a cocinsa a jiya.

Suleman yace shugaban kasa Igbo mai yiwuwa ya kasance shine maganin matsalar mu a Najeriya ta fannin samar da ayyukanyi da kuma tattalin arzikin kasar nan.

Najeriya na bukatar shugaban kasa Igbo - Apostle Suleman

Najeriya na bukatar shugaban kasa Igbo - Apostle Suleman

Yayi jawabin a cocinsa a ranar Lahadi, a helikwatar cocin dake garin Auchi, yace a babban zabe mai zuwa na shugaban kasa ya kamata mu zabi Igbo a matsayin shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Jami’an SARS sun sake kama Dino Melaye

Suleman yace Igbo a kasar nan sunfi kowa yawan ma’aikata da cewa kusan kowane Igbo a kasar nan yana da kasuwanci wanda ke ja afadin kasar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel