Yanzu Yanzu: Jami’an SARS sun sake kama Dino Melaye

Yanzu Yanzu: Jami’an SARS sun sake kama Dino Melaye

Jami’an hukumar yan sanda na SARS sun kama shugaban kwamitin babban birnin tarayya na majalisar dattawa, Dino Melaye, wanda ke wakiltan Kogi West a majalisa.

An rahoto cewa a safiyar yau ne aka tsare Sanata Dino Melaye a hukumarsu dake kallon tsohon babban bankin Najeriya, CBN junction hanyar babban titin Area 1.

An tanadi wannan ofishin nasu ne domin ajiye masu laifi da ke nuna taurin kai bayan an kama su da laifin sata, kisan kai, kungiyar asiri da sauran ayyukan laifi.

Yanzu Yanzu: Jami’an SARS sun sake kama Dino Melaye

Yanzu Yanzu: Jami’an SARS sun sake kama Dino Melaye

An tattaro cewa rundunar sojin Najeriya ta kama Melaye ne ta karfin tuwo ba tare da jiran izini ko umurnin kotu ba.

KU KARANTA KUMA: Rahma Sadau ta caccaki Atiku Abubakar

A kiran tarho da akayi da safen nan, anji wani hayaniya ta kasa wanda ake ganin gwagwarmaya ne tsakaninsa da wasu jami’a wanda daga bisani aka kashe wayar tasa.

Idan zaku tuna a jiya Legit.ng ta kawo cewa an kama Dino a filin jirgin sama na Auja a hanyarsa ta zuwa kasar Morocco, ziyarar aiki.

Sai dai yan sa’o’i bayan nan mun ji cewar an sake shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel