Ina tinanin zan sake tsayawa takarar gwamna - Ganduje

Ina tinanin zan sake tsayawa takarar gwamna - Ganduje

- Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, na shawarar sake tsayawa takarar gwamnan jihar Kano a zabe mai zuwa

- Gwamna Ganduje yace saboda yana so cigaba ya dore a jihar, shiyasa nake tinanin sake tsayawa takara a karo na biyu

- Ganduje yace shekaru hudu basu ishi kowace gwamnati ta aiwatar da gagarumin aikin cigaba ba wanda ya kamata a samu a siyasance ba

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, ya zanta da manema labarai game da zaben 2019 tare da Ladi Akeredolu-Ale, inda ya bayyana shawararsa na sake tsayawa takarar gwamnan jihar Kano a zabe mai zuwa na 2019.

Gwamna Ganduje yace saboda yana so cigaba ya dore a jihar, shiyasa nake tinanin sake tsayawa takara a karo na biyu, musamman ma saboda kira da nake yawan samu daga masoya na shine ma ya kara sanyani tinanin kara tsayawa takara.

Ina tinanin zan sake tsayawa takarar gwamna - Ganduje

Ina tinanin zan sake tsayawa takarar gwamna - Ganduje
Source: Depositphotos

Ganduje yace shekaru hudu basu ishi kowace gwamnati ta aiwatar da gagarumin aikin cigaba ba wanda ya kamata a samu a siyasance ba.

KU KARANTA KUMA: Dandalin Kannywood: Labarin Jaruma Sadiya Adam Idris da baku sani ba

Ganduje yayi jinjina ga shugaban kasa Muhammadu Buhari game da yanda ya shiga cikin lamarin rikicin jam’iyyar tasu ta APC wanda suka fuskanta a ‘yan kwanakinnan. Ya kara da cewa dama ana dan samun kace nace a siyasa ba wani abun damuwa bane.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta ruwaito a baya cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kudirinsa na sake takara a zaben 2019, domin a cewarsa hakan shine ra'ayin yan Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel