Rikita-Rikita: Manyan daraktoci 5 a gwamnatin Buhari za su fuskanci kuliya 14 ga watan Mayu

Rikita-Rikita: Manyan daraktoci 5 a gwamnatin Buhari za su fuskanci kuliya 14 ga watan Mayu

Akalla manyan daraktocin hukumar ado da wasannin kwaikwayo mallakar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari watau National Art Theatre a turance ne za su fuskanci alkali a wata kotun tarayya ta garin Legas a ranar 14 ga watan Mayu.

Kamar dai yadda muka samu, daraktocin za su fuskanci alkalin ne bisa zargin karbar na goro na makudan kudaden da suka kai Naira dubu dari biyar daga hannun wani dan kwangila.

Rikita-Rikita: Manyan daraktoci 5 a gwamnatin Buhari za su fuskanci kuliya 14 ga watan Mayu

Rikita-Rikita: Manyan daraktoci 5 a gwamnatin Buhari za su fuskanci kuliya 14 ga watan Mayu

KU KARANTA: Maganar karin alawus din 'yan NYSC ta kara tasowa

Legit.ng ta samu cewa manyan daraktocin dai sune Ndubuisi Nwogu, George Ufot Ukanta, Abiodun Abe, Femi Joel da kuma Uwar gida Doris Okafor, dake zaman matar wani tsohon Janar a rundunar sojin Najeriya.

A wani labarin kuma, Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu, Sanatocin jam'iyyar adawa ta PDP suna ta shire-shiren tsige shugaban marasa rinjaye kuma tsohon gwamnan Akwa Ibom Sanata Godswill Akpabio daga mukamin sa.

Mun samu dai cewa 'ya'yan jam'iyyar ta PDP sun yanke shawarar ne musamman saboda yadda suka ce ya kasa jagorantar Sanatocin wajen yin adawa da kudurorin gwamnatin APC a zauren majalisar yadda ya kamata.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel