Sanatocin jam'iyyar PDP sun soma shiryawa shugaban marasa rinjaye wata kullalliya

Sanatocin jam'iyyar PDP sun soma shiryawa shugaban marasa rinjaye wata kullalliya

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu, Sanatocin jam'iyyar adawa ta PDP suna ta shire-shiren tsige shugaban marasa rinjaye kuma tsohon gwamnan Akwa Ibom Sanata Godswill Akpabio daga mukamin sa.

Mun samu dai cewa 'ya'yan jam'iyyar ta PDP sun yanke shawarar ne musamman saboda yadda suka ce ya kasa jagorantar Sanatocin wajen yin adawa da kudurorin gwamnatin APC a zauren majalisar yadda ya kamata.

Sanatocin jam'iyyar PDP sun soma shiryawa shugaban marasa rinjaye wata kullalliya

Sanatocin jam'iyyar PDP sun soma shiryawa shugaban marasa rinjaye wata kullalliya

KU KARANTA: Dalilin da ya sa na dawo daga rakiyar Buhari - Atiku

Legit.ng dai ta samu da majiyar ta ta cewa shirin kullalliyar dai an jima ana yin sa watanni da dama da suka shude amma kuma lamarin ya kara daukar sabon salo a kimani sati biyu da suka shude.

A wani labarin kuma, Akalla manyan daraktocin hukumar ado da wasannin kwaikwayo mallakar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari watau National Art Theatre a turance ne za su fuskanci alkali a wata kotun tarayya ta garin Legas a ranar 14 ga watan Mayu.

Kamar dai yadda muka samu, daraktocin za su fuskanci alkalin ne bisa zargin karbar na goro na makudan kudaden da suka kai Naira dubu dari biyar daga hannun wani dan kwangila.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel