Kasar Saudiyya ta saki bam a taron daurin aure, mutane 20 sun mutu

Kasar Saudiyya ta saki bam a taron daurin aure, mutane 20 sun mutu

- Ana zargin kasar Saudiyya da hannu cikin wani harin sama daya halake mutane 20 a kasar Yemen

- Kungiyar 'yan tawayen Houthi ne suka tuhumar kasar Saudiyyar inda suka ce dama gamayar kasashen da Saudiyya ke jagoranta na goyon bayan kasar Yemen

- Mai magana da yawun gamayar kasashen da ake zargi yace za'a gudanar da bincike akan harin

A kalla mutane 20 ne suka rasa rayukan su a wani biki da aka gudanar a yammacin Yemen ciki kuwa harda amaryar sakamakon wani harin sama da aka kai musu.

Mazauna yankin da ma'aikatan lafiya sun bayyana cewa mutane 30 ne sukaji raunuka a harin da akakai a ranar Lahadi a yankin Bani Qais.

Wata harin da Saudiyya ta jagoranta yayi sanadiyar mutuwar mutane 20 a wajen bikin aure

Wata harin da Saudiyya ta jagoranta yayi sanadiyar mutuwar mutane 20 a wajen bikin aure

'Yan tawayen kungiyar Hauthi sun dora laifin harin akan gamayar kasar wasu kasashen karkashin jagorancin Saudiyya wanda ke goyon baya kasar Yemen akan yakin basasa da tayi na shekara uku.

KU KARANTA: A yau zan mika kaina ga jami'an 'Yan sanda - Dino Melaye

Mai magana da yawun gamayar ya ce za'a gudanar da bincike a kan tuhumar duk da cewa gamayar kasashen sun ce baya cikin tsarin su kai hari ga fararen hula da gangan sai dai kungiyoyin kare hakkin bil adama sun zarge su da kai hari a kasuwani, asibitoci, makarantu da gidajen al'umma.

Gidan talabijin na Houthis Almasirah ya bayyana cewa jiragen yakin guda biyu sunkai harin ne a kauyen Al-Raqa wanda yake da tazarara kilomita 90 tsakanin sa da babban birnin Sanaa.

Gidan talabijin din ya bayyana mutum 33 ya kuma hasko gurin da abin ya faru inda wani karamin yaro ke kwance jikin wani mutum yana kuka tare da neman agaji.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel