Tsohon gwamna a Arewa ya sha tambayoyi wurin hukumar EFCC kan badakalar Naira biliyan 2

Tsohon gwamna a Arewa ya sha tambayoyi wurin hukumar EFCC kan badakalar Naira biliyan 2

Labarin da muke samu sun tabbatar mana da cewa hukumar nan da ke yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta gwamnatin tarayya watau Economic and Financial Crimes Commission, EFCC ta tutse tsohon gwamnan jihar Filato har na tsawon awayi bakwai.

Mun samu haka zalika cewa hukumar ta EFCC ta matsi Sanatan da yanzu haka yake wakiltar mazabar jihar Filato ta Arewa ne bisa zargin almundahana na zunzurun Naira biliyan biyu na kudaden al'umma.

Tsohon gwamna a Arewa ya sha tambayoyi wurin hukumar EFCC kan badakalar Naira biliyan 2

Tsohon gwamna a Arewa ya sha tambayoyi wurin hukumar EFCC kan badakalar Naira biliyan 2

KU KARANTA: Sanata Shehu Sani ya kwantowa El-Rufai kura a kotu

Legit.ng ta samu dai cewa tsohon gwamnan ya je ofishin hukumar ta EFCC din ne wajen karfe 11 na safe amma bai bar ofishin ba har sai karfe 6 na yammar ranar Litinin din da ta gabata.

A wani labarin kuma, Fitaccen dan majalisar dattijan nan dake wakiltar mazabar jihar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya maka gwamnan jihar ta Kaduna a gaban wata babbar kotun jihar inda ya nemi diyyar batancin da yace gwamnan yayi masa har ta Naira biliyan 5.

Mun samu cewa Sanatan dai ya yi wannan rokon ne a matsayin martani ga wata kara da gwamnan ya shigar akan shi a watannin baya inda ya nemi diyyar Naira miliyan 500 daga Sanatan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel