Al'amurran tsaro 5 da suka bukaci Shugaba Buhari ya kawo ƙarshen su a Najeriya

Al'amurran tsaro 5 da suka bukaci Shugaba Buhari ya kawo ƙarshen su a Najeriya

Duk da taka-tsan-tsan na matakan tsaro da gwamnatin Najeriya ke ganiyar ta wajen faman gindayawa a kasar nan, har yanzu ta na ci gaba da fuskantar barazana da kuma kalubalai da suka ci suka ki cinyewa.

Al'amurran tsaro 5 da suka bukaci Shugaba Buhari ya kawo ƙarshen su a Najeriya

Al'amurran tsaro 5 da suka bukaci Shugaba Buhari ya kawo ƙarshen su a Najeriya

A sanadiyar haka ya sanya jaridar Legit.ng cikin binciken shafin Daily Trust ta kalato wasu muhimman kalubalai na tsaro da suka sha gaban shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Rahotanni da sun bayyana cewa, ko a makon da ya gabata shugaba Buhari yayin ganawa a birnin Landan da Firai Ministar kasar Ingila Theresa May, ya bayyana cewa babban kalubalen da yafi ci ma shi tuwo a kwarya a hanlin yanzu shine matsalolin tsaro sa'annan tattalin arziki.

Hasashe ya bayyana cewa wannan kalubai na iya kasancewa barazana da za ta kawo tangarda ga shugaba Buhari wajen muradin sake neman kujerar sa ta shugaban kasa a zaben 2019.

Wannan kalubalai na tsaro a kasar Najeriya a halin yanzu da jaridar Legit.ng ta tattaro sun hadar da:

1. Ta'ddancin Boko Haram

Musamman a yankin Arewa Maso Gabashin kasar nan, Najeriya tana fama da tashin hankali na ta'addancin Boko Haram yayin da har yanzu ake zuba idanu wajen ganin an ceto 'yan Matan Chibok. Sai dai an samu nasarar cin galaba da babban kaso akan 'yan ta'addan tun hawan shugaba Buhari mulki a kasar.

2. Rikicin Makiyaya da Manoma

Har yanzu rikici a tsakanin makiyaya da manoma ya ki ci ya ki cinyewa tun kisan mutane 73 a kananan hukumomin Guma Logo na jihar Benuwe tun a ranar 1 ga watan Janairu na shekarar 2018.

Kawowa yanzu rikicin ya ci gab da ta'azzara musamman a jihohin Benuwe, Nasarawa da kuma Taraba.

3. Garkuwa da Mutane:

Garkuwa da mutane gami da karbar kudin fansar su ya ci gaba da ta'azzara kasar nan wanda a halin yanzu yana daya daga cikin kalubalai na tsaro da suka sha gaban hukumomin tsaro.

KARANTA KUMA: Wani 'Dan Kasuwa ya caccaki Keyamo kan batun amincewa da yiwa Shugaba Buhari hidima

4. Fashi da makami gami da sara suka

Musamman fashin da makami na garin Offa dake jihar Kwara a kwana-kwanan nan ya zamto abin gudana a harsunan al'umma inda kimamin rayuka 20 suka salwanta.

Akwai kuma 'yan sara-suka ta ci gab da cin karen su ba bu babbaka musamman a jihar Zamfara dake Arewa maso Yammacin kasar nan.

5. Tashin-Tashina da 'Yan Shi'a

Rikici tsakanin shi'a da hukumomin tsaro a kasar ya dauki wani sabon salo yayin da suke gudanar da zanga-zanga da tayar da kayar baya a sakamakon ci gaba da tsare shugaban kungiyar shi'a na Najeriya, Ibrahim El-Zakzaky da gwamnati ke ci gaba da yi tun damkar sa a watan Dasumba na shekarar 2015.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel