Zabukan 2019 za su yamutsa hazo - Shugaban jam'iyyar APC, Oyegun

Zabukan 2019 za su yamutsa hazo - Shugaban jam'iyyar APC, Oyegun

Shugaban jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress, APC na kasa baki daya mai suna Cif John Odigie-Oyegun ya gargadi sauran 'ya'yan jam'iyyar ta su da su shirya gumurzu mai zafi a zaben 2019 mai zuwa domin kuwa ba zai zo da sauki ba.

Haka zalika ma dai Cif Oyegun ya kuma bayyana cewa duk da cewa dai har yanzu jam'iyyar su tana da matukar karfi kuma da ran ta, to amma fa dole ne sai shugabanni da kuma 'ya'yayen ta sun kara zage damtse indai har suna so suyi nasa.

Zabukan 2019 za su yamutsa hazo - Shugaban jam'iyyar APC, Oyegun

Zabukan 2019 za su yamutsa hazo - Shugaban jam'iyyar APC, Oyegun

KU KARANTA: Dalilin da ya sa na bar tafiyar Buhari - Atiku

Legit.ng ta samu dai cewa Cif Oyegun din ya dai yi wannan bayanin ne a lokacin da yake kaddamar da kwamitin gudanar da zabukan jam'iyyar a matakin kasa a karkashin jagorancin gwamnan Jigawa a garin Abuja.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa tuni dai jam'iyyar ta APC ta fitar da jadawalin zabukan shugabannin ta a matakai na mazabu da rumfuna har zuwa jihohi da kuma kasa baki daya bayan takaddamar da aka samu a watannin baya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel