Dalilan da ya sa na dawo daga rakiya Shugaba Buhari – Atiku Abubakar

Dalilan da ya sa na dawo daga rakiya Shugaba Buhari – Atiku Abubakar

Fitaccen dan siyasar nan kuma tsohon Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana cewa yana da dalilai masu tari yawa da suka sanya ya dawo daga rakiyar Shugaba Muhammadu Buhari.

Mun samu cewa Atiku din ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da wakilin majiyar mu biyo bayan wata tattaunawa da yayi da yayi lokacin ziyarar zuwa ofishin BBC da ke Landan ranar Litinin.

Dalilan da ya sa na dawo daga rakiya Shugaba Buhari – Atiku Abubakar

Dalilan da ya sa na dawo daga rakiya Shugaba Buhari – Atiku Abubakar

KU KARANTA: An kashe babban malamin addini a A=wajen taron APC a arewa

Legit.ng ta samu cewa Atikun da yanzu yake zaman jigo a jam'iyyar adawa ta PDP ya ce "bayan da Shugaba Buhari ya kama mulki jam'iyyar APC ta fara tafiya ne a gurgunce."

Haka zalika ya kuma bayyana cewa ya lura cewa shawarwarin da ya bayar ga shugaban ba su yi wani tasiri ba shi yasa yaga ya kamata ya sauya shekar.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a watan Disamabar shekarar da ta shude ne bara ne Atiku Abubakar din ya fice daga jam'iyya mai mulki ta APC, inda daga bisani ya koma jam'iyyar hamayya ta PDP.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel