Ba gaskiya ba ne Mai martaba yace na guji taro a Birtaniya don wani aiki ya kai mu Amurka - Kachiwku

Ba gaskiya ba ne Mai martaba yace na guji taro a Birtaniya don wani aiki ya kai mu Amurka - Kachiwku

- Ministan fetur yayi karin haske game da abin da ya faru a makon nan

- Sarki Sanusi II yayi tir da Ministocin Buhari na kin halartar wani taro

- Ibe Kachikwu yace a lokacin da aka yi taron shi ma yana wani aiki a US

Karamin Ministan man fetur na Gwamnatin Shugaba Buhari ya maidawa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II martani na cewa Ministocin kasar ba su halarci wani muhimmin taro da aka yi ba a Landan kwanan nan.

Ba gaskiya ba ne Mai martaba yace na guji taro a Birtaniya - Kachiwku

Kachiwku yace wani taro a Amurka ya hana shi zuwa Ingila

Sai dai Ministan fetur din na Najeriya yayi wa Mai martaba Sanusi II raddi inda ya bayyana cewa lokacin da aka yi taron yana Kasar Amurka ba Ingila ba. A baya Sarkin yace Ministocin su na Ingila amma ba su je taron ba.

Emmanuel Ibe Kachikwu ta bakin Idang Alibi wanda shi ne Jami’in sa na yada labarai yace Ministan ya halarci wani taro ne a Amurka mai matukar muhimmanci ga cigaban kasar tare da wasu manya a Gwamnatin Najeriya.

KU KARANTA:

A baya dai Sarkin Kano kuma tsohon babban Bankin Najeriya Sanusi Sanusi yayi tir da Ministocin Buhari da yace sun yi sake bas u halarci taon da aka yi a Kasar Birtaniya ba wanda zai iya jawowa Najeriya asarar dinbin albarka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel