Kallon fim din batsa ya saka shi yiwa mahaifiyar sa fyade

Kallon fim din batsa ya saka shi yiwa mahaifiyar sa fyade

Wani matashi mai mayatar kallon fina-finan batsa ya shiga hannun hukuma bayan ya yiwa mahaifiyar sa fyade a kasar Indiya.

Matashin, Rohan; mai shekaru 22, ya lallaba dakin mahaifiyar sa da tsakar dare tare da daure mata baki yayin da take kwance tana bacci.

Bayan mahaifiyar sa ta farka sai Rohan ya wayance da cewar yana neman ruwa ne kafin daga bisani ya haike mata.

Makwabtan su sun ce sun ji ihun mahaifiyar matashin a yayin da take kokarin neman taimako, sai dai makwabtan basu kira 'yan sanda ba saboda yawan samun fada a gidan.

Kallon fim din batsa ya saka shi yiwa mahaifiyar sa fyade

Kallon fim din batsa ya saka shi yiwa mahaifiyar sa fyade

Makwabtan su sun tabbatar da cewar Rohan na yawan kallon fim din batsa a wayar sa.

Kazalika 'yan sanda sun ce Rohan kan raba dare yana kallon fim din batsa, wasu lokutan ma a gaban mahaifiyar sa da 'yar uwar sa.

DUBA WANNAN: Zan yi dokar datse hannun duk wanda aka samu da laifin sata - Dan takarar shugaban kasa

Mahifiyar sa ta sanar da mijin ta da babban dan ta kafin daga bisani su shigar da korafi a ofishin 'yan sanda. Kazalika, ta sanar da 'yan sanda cewar ya sha yunkurin haike mata a baya.

Jami'in 'yan sanda, S M Rabari ya ce: "Mun kama Rohan kuma mun aika shi da mahaifiyar sa asibiti domin gwaji."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel