Zan yi dokar datse hannun duk wanda aka samu da laifin sata - Dan takarar shugaban kasa

Zan yi dokar datse hannun duk wanda aka samu da laifin sata - Dan takarar shugaban kasa

A yayin da zaben shugaban kasa ke kara karatowa a kasar Mexico, daya daga cikin 'yan takarar ya bayyana cewar datse hannun barayi ne kadai hanyar da za a bi domin rage sata a kasar.

Kalaman dan takarar mai zaman kan sa, Jaime Rodriguez, da aka fi kira da "El Bronco", ya jawo cece-kuce a shafin sa na Tuwita dake dandalin sada zumunta.

"Ya kamata mu fara datse hannun duk wanda aka samu da laifin sata da fashi. Abu ne mai sauki, zan tura dokar majalisa ne kawai da zarar na zama shugaban kasa," kamar yadda El Bronco ya rubuta a Tuwita.

Kalaman na dan takarar ya matukar kidima jama'a har ta saka sun sake tambayar sa domin tabbatar da abinda suka karanta amma ya kara maimaita masu cewar hakan fa yake nufi.

Zan yi dokar datse hannun duk wanda aka samu da laifin sata - Dan takarar shugaban kasa

Zan yi dokar datse hannun duk wanda aka samu da laifin sata - Dan takarar shugaban kasa

Duk da bai ambaci sunan wata kasa ba, dan takarar ya bayyana cewar kasashe da dama saida suka yi hakan kafin su iya rabuwa da matsalar cin hanci.

Kasashen Saudiyya da Iran na daga cikin kasashen da ke zartar da hukuncin datse hannu ga barayi.

DUBA WANNAN: Hukumar EFCC zata koma sabon ofishin ta da aka gina a kan biliyan N24bn

Rahotanni sun bayyana shakku a kan dokar tare da tambayar a kan wadanda dokar zata yi aiki; masu mulki ko talakawa.

An fara zaben El Bronco a matsayin gwamna a matsayin dan takara mai zaman kan sa a 2015, matsayin da ya ajiye domin yin takarar shugaban kasa.

El Bronco na mataki na biyar a zaben jin ra'ayin jama'a a kan 'yan takarar dake neman shugabancin kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel