Dubun yan bindigar da suka kashe Dansandan dake gadin gonar Magu ta cika

Dubun yan bindigar da suka kashe Dansandan dake gadin gonar Magu ta cika

Rundunar Yansandan Najeriya ta sanar da kama wasu Yan bindiga guda uku da suka kashe wani Dansanda dake gadin gonar shugaban hukumar yaki da rashawa, EFCC, Ibrahim Magu, dake garin Karshi, na jihar Abuja.

Mataimakin Kaakakin rundunar Yansanda, SP Aremu Adeniran ne ya sanar da haka a ranar Litinin 23 ga watan Afrilu a babban birnin tarayya Abuja, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

KU KARANTA: Zamba cikin aminci: wata Mata mai shekaru 39 ta saci jaririyar makwabciyarta

Majiyar Legit.ng yan bindgar sun kai harin ne a ranar 12 ga watan Disamba na shekarar 2017, a dalilin haka suka bindige Sajan Haruna Sarki, jami’in Dansandan dake gadin gonar.

Kaakakin yace rundunar Yansanda ta musamman dake karkashin ikon babban sufetan Yansandan Najeriya ne suka kama su, daga cikin yan bindigar akwai tsofaffin jami’an rundunar Sojan kasa da aka sallama daga aiki, kuma an kwato bindigu guda biyu kirar AK 47, Alburusai da wayoyi guda biyu.

Daga karshe Kaakakin yace zasu mika Sojojin guda biyu ga hukumar Yansanda, sa’annan yace zasu cigaba da farautar sauran yan bindigar, tare da gurfanar dasu gaban Kotu.

Bugu da kari Kaakakin ya bada tabbacin manufar rundunar Yansandan Najeriya na magance aikata manyan laifuka, tare da kare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel