Yanzu-yanzu: Rikici ya sake ballewa tsakanin yan sanda da yan Shi'a a ikin garin Abuja

Yanzu-yanzu: Rikici ya sake ballewa tsakanin yan sanda da yan Shi'a a ikin garin Abuja

Jami'an yan sandan babban birnin tarayya, ta kuma cakumewa da mabiya Sheik Ibrahim Zakzaky da aka fi sani da yan Shi'a masu zanga-zanga a babban birnin tarayya Abuja.

Masu zanga-zanga sun yi rikici da jami'an tsaron ne a unguwar Maitama inda suka jifan yan sandan. Wannan jefe-jefe ya shafi dukiyoyin jama'a mazauna unguwar wanda ya kunshi motoci da gidajensu.

Su kuma jami'an yan sandan sun tarwatsasu da barkonon tsohuwa

Legit.ng dai ta samu cewa a cikin masu zanga-zangar hadda mata, kananan yara da kuma matasa hadi da shugabannin 'yan shi'ar daga sassa daban daban na fadin kasar.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa gwamnatin ta tarayyar Najeriya karkashin shugabancin Muhammadu Buhari ce ke cigaba da tsare shugaban 'yan shi'ar Sheikh Ibrahim Zakzaky biyo bayan wata arangaba da mabiyan sa suka yi da jami'an tsaro a shekarar 2015.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel