Saraki da Tambuwal bazasu bar APC ba - Gwamna Badaru

Saraki da Tambuwal bazasu bar APC ba - Gwamna Badaru

- Gwamna Abubakar Badaru na Jigawa yace ba gaskiya bace jita-jitar da akeyi cewa shugaban Majalisa Bukola Saraki da Gwanan jihar Sokoto wai zasu bar jam’iyyar APC

- Gwamna Badaru ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da shugaban ma’aikata na shugaban kasa a fadar shugaban kasar cewa ba rikici bane akayi a lokacin zagayen jam’iyyar

- Gwamna Badaru yace wannan zagayen za’a yishi cikin kwanciyar hankali saboda duk sansanin dake akwai na magoya bayan jami’iyyar sun hada kawunansu yanzu

A ranar Litinin ne Gwamna Abubakar Badaru na Jigawa yace ba gaskiya bace jita-jitar da akeyi cewa shugaban Majalisa Bukola Saraki da Gwanan jihar Sokoto wai zasu bar jam’iyyar APC.

Gwamna Badaru ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da shugaban ma’aikata na shugaban kasa a fadar shugaban kasar cewa ba rikici bane akayi a lokacin zagayen jam’iyyar, kawai kace nace tsakaninin magoya bayan ‘yan takara daban daban na jam’iyyar.

Saraki da Tambuwal bazasu bar APC ba - Gwamna Badaru

Saraki da Tambuwal bazasu bar APC ba - Gwamna Badaru

Gwamna Badaru yace wannan zagayen za’a yishi cikin kwanciyar hankali saboda duk sansanin dake akwai na magoya bayan jami’iyyar sun hada kawunansu yanzu. Yace “muna fatan wannan karon za’ayi zagayen cikin kwanciyar hankali da lumana.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Jami’an ‘Yan Sanda rike da makamai sun mamaye gidan Dino Melaye na birnin tarayya

Yace “har yanzu muna tare da gwamna Aminu Tambuwal da kuma shugaban majalisa Bukola Saraki, duk suna nan a jam’iyyar APC, saboda babu dalilin da zaisa muyi tinanin cewa suna kokarin daidaitawa da ‘yan wata jam’iyya,.”

A halin da ake ciki Legit.ng ta rahoto cewa Bukola Saraki da Tambuwal da wasu tsofaffin ‘yan jam’iyyar sun bawa jam’iyyar ta PDP ka’idar canja suna kafin su amince su koma jam’iyyar gabannin zaben shekara mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel