Babu wani wanda Buhari zai bawa hakuri don yace wasu Matasan Najeriya cima zaune ne – Tony Momoh

Babu wani wanda Buhari zai bawa hakuri don yace wasu Matasan Najeriya cima zaune ne – Tony Momoh

- Murnar Matasan dake sa ran Buhari zai ba su hakuri ta koma ciki

- Don wani jigo a APC yace bai ga dalilin bayar da hakurin ba, tunda za'a zuba jarin biliyoyin dalolin da zasu samawa Matasa aikin yi

Tsohon Ministan yada labarai kuma shugaban hukumar gudanarwar jami’ar Jos ya bayyana cewa, bai ga dalilin da yasa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bawa wani hakuri ba, don y ace mafi yawan Matasan Najeriya kasalallu ne kuma basu da aiki.

Babu wani wanda Buhari zai bawa hakuri don yace wasu Matasan Najeriya cima zaune ne – Tony Momoh

Babu wani wanda Buhari zai bawa hakuri don yace wasu Matasan Najeriya cima zaune ne – Tony Momoh

Momoh wanda jigo ne a jam’iyyar APC ya bayyana hakan ne yayin hirarsa da jaridar DAILY INDEPENDENT, a matsayin martani ga wadanda suke kira ga shugaba Buharin ya nemi afuwar Matasan Najeriya bisa kalaman da yayi yayin taron kasashe rainon Ingila.

A cewarsa, shugaba Buharin ko kadan baya nufin duk matasan Najeriya kasalallu ne, sai dai abinda yake nufi shi ne, da yawa daga cikin Matasan ba su da aikin yi suna zaune ne a gida suna jiran tsammani. Kuma shi Buhari ko yaushe yana fadar abinda yake zuciyarsa ne baya karya, ba kamar yan siyasar da suka kware wajen fadawa mutane abinda zai faranta musu rai kawai ba ne.

KU KARANTA: Kutungwiwar Majalisa: Allah sarki karshen Magu yazo a matsayin shugaban EFCC

“Ya nemi afuwa, afuwar me? Maganar da ya fada ba haka take ba ne? ba gaskiya bane Matasan Najeriya ba su da aiki ba? Mai yasa zai nemi afuwa don ya fadi gaskiya” Momoh ya tambaya cikin daurewar kai.

Tsohon Ministan ya kara da, Najeriya nada Matasa masu tarin yawa, shin daga cikin masu aiki da yan zaman kashe wando suwa suka fi yawa? Tabbas mara sa aiki ne, kaga kennan gaskiya ya fada.

Kamfanin Shell zai sanya jarin $15b, yanzu wannan ba'a bin ayi murna bane? Yan Najeriya da yawa zasu samu aikin yi.

Idan za'a yi maganar da ta dace, tsakanin maganganun da yayi biyu, a dora a ma’auni, ni ina ganin batun zuba jarin $15b yafi wannan maganar ta cewa wai shugaba Buhari yace Matasan Najeriya kasalallu ne da suke maitar son a basu komai kyau.

Kuma yan siyasa ne suke murda zance da yayi, gaba daya daga farkon maganarsa babu inda yace kasalallu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel