Buhari ya gaza, ya yi mana alkawarin zuma, ya bamu madaci – Inji Sanata

Buhari ya gaza, ya yi mana alkawarin zuma, ya bamu madaci – Inji Sanata

Wakilin al’ummar mazabar jihar Bayelsa ta gabas a majalisar wakilai, Sanata Ben Bruce Murray ya bayyana cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza matuka a shayar da yan kasa romon dimukradiyya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sanata Murray yayi wannan bayani ne a yayin da yake raddi ga maganan da ake yamadidin na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zargi matasan Najeriya da lalaci da zaman banza.

KU KARANTA: Za’a kashe dala miliyan 322 daga kudin da Abacha ya sata akan talakawa da gajiyayyu

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sanatan yana cewa shugaban kasa Buhari ya manta da cewa matasan dayake zargi da lalaci ne suka zabe shi ta hanyar bashi kuri’u da dama.

Buhari ya gaza, ya yi mana alkawarin zuma, ya bamu madaci – Inji Sanata

Bruce da Buhari

“A maimakon ya samar ma matasan Najeriya aikin yi, tare da gana musabbabin ficewarsu kasashen Turai amma sai gas hi ya buge da zaginsu, yana kiransu malalata. Abin mamakin ma shi ne da damansu sun bi dogon layi, a cikin rana don su zabe, shi. Amma sai ga shi yanzu ya bamu madaci, bayan yayi alkawarin bamu zuma.” Inji shi.

Sai dai Kaakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina ya musanta zargin cewa shugaban kasa ya bata sunayen matasan Najeriya, inda yace babu yadda za’ayi Buhari yayi hakan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel