Yanzu Yanzu: Jami’an ‘Yan Sanda rike da makamai sun mamaye gidan Dino Melaye na birnin tarayya

Yanzu Yanzu: Jami’an ‘Yan Sanda rike da makamai sun mamaye gidan Dino Melaye na birnin tarayya

- Bayan awowi kadan da ya samu sake daga hannun jami’an kula da ‘yan gudun hijira a filin jirgi na Nnamdi Azikiwe, jami’an ‘Yan Sanda suka mamaye gidan Sanatan Dino Melaye

- A yanzu haka akwai motoci hudu cike da ‘Yan Sanda sun mamaye hanyar Mississippi, a Maitama dake birnin tarayya

Bayan awowi kadan da ya samu sake daga hannun jami’an kula da ‘yan gudun hijira a filin jirgi na Nnamdi Azikiwe, jami’an ‘Yan Sanda suka mamaye gidan Sanatan Dino Melaye.

Majiyarmu sunce a yanzu haka akwai motoci hudu cike da ‘Yan Sanda sun mamaye hanyar Mississippi, a Maitama dake birnin tarayya.

Jami’an ‘Yan Sandan sunki amincewa suyi wani jawabi game da lamarin kuma sun hana jami’in labarai daukar hotuna a wurin.

Yanzu Yanzu: Jami’an ‘Yan Sanda rike da makamai sun mamaye gidan Dino Melaye na birnin tarayya

Yanzu Yanzu: Jami’an ‘Yan Sanda rike da makamai sun mamaye gidan Dino Melaye na birnin tarayya

A baya Legit.ng ta rahoto cewa an kama Sanata Dino Melaye mai wakiltan Kogi West a filin jirgin sama na Abuja.

KU KARANTA KUMA: Ina fatan kada Allah yasa Najeriya ta sake fuskantar yakin basasa - Gowon

A cewar wani rubutu da Sanatan ya wallafa a shafinsa na Twitter a safiyar ranar Litinin, 23 ga watan Afrilu, sanatan yace an kama shi ne a hanyarsa ta zuwa Morocco domin ziyarar aiki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel