An gurfanar da dan shekara 40 da ya yiwa wasu daliban firamare uku fyade a Katsina

An gurfanar da dan shekara 40 da ya yiwa wasu daliban firamare uku fyade a Katsina

Wani mutum mai shekaru 40, Abdullahi Umar, ya gurfana gaban kotun majistare dake Katsina bisa tuhumar yiwa wasu daliban makarantar firamare uku fyade.

Yanzu haka Umar, lebura, dake zaune a unguwar Dan'rimi dake karamar hukumar Malumfashi a Katsina na tsare a gidan yari bisa umarnin kotu.

Hukumar 'yan sanda ta gurfanar da shi a gaban kotun bisa tuhumar sa da aikata fyade, laifin da ya sabawa sashe na 283 na kundin fenal kod.

An gurfanar da dan shekara 40 da ya yiwa wasu daliban firamare uku fyade a Katsina

An gurfanar da dan shekara 40 da ya yiwa wasu daliban firamare uku fyade a Katsina

Shugaban makarantar firamaren Sallau dake Malumfashi, Umar Mohammed, ne ya shigar da korafi a ofishin hukumar 'yan sanda dake Malumfashi a ranar 10 ga watan Afrilu.

Shugaban makarantar ya shaidawa 'yan sanda cewar, sau uku Umar na amfani da kudi domin yaudarar yaran makarantar yana lalata da su a gidan sa.

DUBA WANNAN: Hukumar EFCC zata koma sabon ofishin ta da aka gina a kan biliyan N24bn

'Yan sanda sun shaidawa kotun cewar wanda ake tuhumar ya amsa laifin sa yayin tuhuma tare da shaidawa kotun cewar dama ya taba aikata irin wannan laifin a shekarar 2015.

Dan sanda mai gabatar da kara, Insufekta Sani Ado, ya sanar da kotun cewar har yanzu suna cigaban da binciken mai laifin.

Alkaliyar kotun, Hajiya Fadile Dikko, ta daga sauraron karar tare da bayar da umarnin tsare Umar a gidan yari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel