Yadda aka kama masu fashin Offa: Ta hanyar budurwansu aka cafke su

Yadda aka kama masu fashin Offa: Ta hanyar budurwansu aka cafke su

- 'Yan sanda sun bayyana kama mutane 12 da ake zargi da fashi da makamin da akayi wa banki a Offa, jihar Kwara ta wayoyin da suka kwace daga wadanda abin ya shafa

- Jaridar Vanguard ta bayyana cewa, wadanda ake zargin sun tafi da wayoyin wadanda fashin ya ritsa dasu, wanda daga baya suka ba 'yammatansu

- Ma'aikatan bankin ma sun ba ma' yan sanda duk wayoyin hannun da aka gani a harabar bankin bayan fashin

Yadda aka kama masu fashin Offa: Ta hanyar budurwansu aka cafke su

Yadda aka kama masu fashin Offa: Ta hanyar budurwansu aka cafke su

An bayyana cewa samun kama da aka bawa wayoyin ya sa an kama wadanda ake zargi a Ibadan, Legas da Abeokuta.

Karin bincike ya nuna cewa wadanda ake zargi sun taba zaman gidan yari so da yawa kuma sun kware a harkar.

Wasu 'yan sanda sun fada ma Vanguard cewa masu hotel din da' yan fashin suka sauka sun sanar hukumar 'yan sanda sakamakon samun su da sukayi da abubuwan ta'addanci a lokacin da suke shiga hotel din.

Shugaban hukumar ' yan sandan da shugaban binciken laifuka sun tura jami'an su don bincike. A maimakon su kama wadanda ake zargi, jami'an 'yan sandan sai suka karbi N400, 000 a matsayin cin hanci.

Da suka koma sai suka sanar da shuwagabannin su cewa' yan yahoo ne ba 'yan fashi ba kamar yanda hukumar hotel din ta fada. A washegarin ranar ne' yan fashin suka kai ziyara ga ofishin 'yan sandan inda suka kashe mutane 9 don fanshe kudin su da suka karba.

DUBA WANNAN: Miliyoyin mutane basu sami karbar kuri'unsu ba

A satin da ya gabata ne Hukumar yan sanda da DCO suka gurfanar da mai hotel din da zargin hadin bakin shi gurin kai harin.

Majiyar mu ta fada wa jJaridar Vanguard cewa a take mai hotel din yace ma DPO da DCO su musa cewa in bai sanar dasu ba lokacin da 'yan ta' addan suka sauka a hotel dinshi kafin suyi fashin bankin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel